Gobarar daji ta yi ajalin mutane 42 a Aljeriya

Gobarar daji ta yi ajalin mutane 42 a Aljeriya

Gwamnatin Aljeriya ta bayyana cewa, mutane 42 da suka hada da sojoji 25 ne suka rasa rayukansu sakamakon gobarar dajin da ta kama a kasar.

A jawabin da Firaministan Aljeriya Aiman bin Abdurrahman ya yi ta kafar talabijin din kasar ya bayar da bayanai game da gobarar daji da ke ci gaba da ci a yankunan kasar daban-daban.

Bin Abdurrahman ya shaida cewa, gobarar dajin ta yi ajalin mutane 42 da suka hada da sojoji 25.

Firaministan na Aljeriya ya bayyana suna tattaunawa don dakko hayar jiragen sama na kashe gobara daga kasashen Turai.

Kamfanin dillancin labarai na Aljeriya APS ya sanar da cewa, gobara 103 ta kama a dazukan jihohi 17 da ke kasar.

Ministan Harkokin Cikin Gida na Aljeriya Kamil Biljud ya ce, akwai yiwuwar yin zagon kasa wajen cinna gobarar a lokaci guda, ana gudanar da bincike inda za kuma a hukunta duk wadanda aka samu da hannu a ciki.


News Source:   ()