A Yamai Babban Birnin Jamhuriyar Nijar, dalibai kimanin 20 ne suka rasa rayukansu sakamakon gobarar da ta kama a makarantarsu.
Azuzuwa 21 ne suka kama da wuta a lokaci guda inda dalibai 20 da ba su iya guduwa ba suka rasa rayukansu.
Ana binciken musabbabin tashin gobarar wadda 'yan kwana-kwana suka dauki lokaci mai tsawo kafin su iya kashe ta.
A alkaluman Cigaba na Majalisar Dinkin Duniya, Nijar ce kasar da ta fi kowacce kasa talauci a duniya. Wannan matsala na shafar bangaren ilimi.
Dubunnan azuzuwa an yi su da kiraruwa. Haka zalika akwai yankunan da babu azuzuwan inda dalibai su ke zama a waje ko a karkashin bishiyu don daukar darussa.