Gobara: Najeriya ta yi asarar rayuka 100 da kuɗi N67.1bn a 2024

Gobara: Najeriya ta yi asarar rayuka 100 da kuɗi N67.1bn a 2024

Hukumar ta kuma ce an ceto rayuka al’umma 30,890 da kadarorin da darajarsu ta kai N1.94tr daga ɓarnar da aka samu a lokacin ɓarkewar gobara daban-daban a faɗin ƙasar nan a shekarar 2024.

Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa, Abdulganiyu Jaji ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Abuja ranar Juma’a.

Ya ce, “A shekarar 2024, hukumar kashe gobara ta yi nasarar ceto dukiyoyin da darajarsu ta kai Naira tiriliyan 1.94 tare da yin asarar dukiyoyi da aka yi ƙiyasin ta kai ta Naira biliyan 67.1.

“A cikin wannan shekarar, Hukumar kashe gobara ta kai ɗauki kashe gobara da sauran abubuwan gaggawa inda aka ceto rayuka 30,890 yayin da mutane 23 suka rasa rayukansu. A matsayinmu na ’yan Najeriya, muna cikin waɗanda ke jajantawa iyalan waɗanda suka rasu da kuma ‘yan uwansu.”

Ya danganta yawancin abubuwan da suka faru da sakaci da rashin bin ƙa’idojin kariya.

Jaji ya buƙaci ‘yan Najeriya da su ƙara taka tsantsan a lokacin bazara, inda ya ƙara da cewa haɗarin gobara yana da yawa a wannan kakar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)