A watanni 2 da suka gabata giwaye sama da 350 ne suka mutu a kasar Bostawana da ke Kudancin Afirka.
An samu jikkunan matattun giwayen sama da 350 a yankin Okawango Delta. Gwamnati ta ce babu wanda ya san musabbabin mutuwar giwayen.
Bostawana ce ke da kaso 1 bisa 3 na giwayen da ke Adirka wadanda da ma adadinsu na karewa.
An fara gudanar da bincike don gano musabbabin mutuwar giwayen.