Ghana ta soke karbar takardun biza kafin shiga ƙasar

Ghana ta soke karbar takardun biza kafin shiga ƙasar

Wannan na iya zama daga cikin matakai na ƙarshe da shugaba Akufo-Addo zai aiwatar kafin ya mika mulki ga zaɓaɓben shugaban ƙasar, John Dramani Mahama a ranar 7 ga Janairun da ke tafe.

Shirin ƙasar ta Ghana dai ya zo dai-dai da muradin ƙungiyar tarayyar ƙasashen Afirka, wadda ta shafe shekaru tana ƙoƙarin ƙulla yarjejeniyar zirga-zirgar bai-ɗaya ba tare da biza ba a tsakanin ƙasashe mambobinta, burin da har yanzu ba ta cimma nasara akai ba.

Wasu alƙaluma da bankin raya Afirka ya fitar sun nuna cewar kawo yanzu kashi 28 cikin 100 kawai aka samu nasarar aiwatarwa kan manufar tabbatar da zirga-zirgar bai - ɗaya a tsakanin ƙasashen Afirka.

A halin yanzu dai ƙasashen Rwanda da Benin da Seychelles, da kuma Gambiya ne kawai suka bai wa ‘yan sauran ƙasashen Afirka damar shiga cikinsu ba tare da takardun Biza ba.

A baya dai wani rahoto da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Ghana ta fitar a shekarar 2021 ya nuna cewa a kusan zirga-zirgar jiragen saman Ghana 220,000 daga cikin Afirka, kashi 55 na samu ne daga Afirka ta Yamma inda tuni ake samun shige da fice ba tare da biza ta ECOWAS ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)