Ghana ta haramtawa kamfanonin fansho zuba hannun jari a ƙetare

Ghana ta haramtawa kamfanonin fansho zuba hannun jari a ƙetare

Bayan kwaskwarima da aka yiwa dokar fansho ta shekarar 2010 a ƙasar kamfanonin inshora sun sami damar zuba hannun jari a ƙasashen ƙetare,  a wani yunƙuri na juya kuɗin ma’aikatan, sai dai kuma a yanzu gwamnatin ta hango haɗari game da hakan.

Ƙididdiga ta nuna cewa a yanzu haka akwai kuɗaɗen ma’aikata sama da biliyan 78.2 a hannun irin waɗannan kamfanonin akalla guda 39 da suke juya su a ƙetare.

To sai dai kuma wani bincike na daban ya nuna cewa ba duka irin waɗannan kamfanoni ke zuba jari a ƙetare ba, wasu ma na zuba hannun jari ne a kamfanoni mallakin turai da suka zuba jari a cikin ƙasar.

Dokokin Ghana na baya-bayan nan sun ƙunshi baiwa kamfanin Inshora damar zuba kaso biyar na kuɗaɗen da yake riƙe da su a matsayin hannun jari a ƙetare, sai dai kuma ana zargin kamfanonin da wuce makaɗi da rawa.

Tuni dai hukumar kula da kamfanonin fansho ta ƙasar ta fara ɗaukar matakin, ciki kuwa har da manyan kamfanonin fansho guda uku da suka zuba sama da kaso 80 cikin 100 na kuɗaɗen su a ƙetare a farkon shekarar da muke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)