Ghana ta ƙaddamar da masana'antar sarrafa zinare ta farko a ƙasar

Ghana ta ƙaddamar da masana'antar sarrafa zinare ta farko a ƙasar

Wannan masana’antar ta Ghana dai da yiwuwar zata kasance ta biyu a Nahiyar Afirka wajen samar da nagartattun sanda sandar zinare a babbar kasuwar hada hadarsa ta Birtaniya LBMA.

A yayin bude masana’antar ta Ghana Gold Refinery mataimakin shugaban kasar Ghanan ne Mahamudu Bawumia ya kaddamar dashi a Accra babban birnin kasar, wanda zai kasance mai taka rawa a fagen bunkasa tattalin arzikin kasar.

Babban bankin Ghana ne tare da hadin gwiwar wani kamfanin sarrafa ma’adanai suka kafa shi da zummar ba da tasu gudun mawa ga kokarin da gwamnatin ke yi wajen farfado da tattalin arzikin kasa tare da samar da ayyukan yi.

Sannan masana’antar na da karfin da zai tace akalla tan dari da ashirin a shekara, wadda zai wadata bukatar da kasar ke dashi na ma’adanin na karkashin kasa mai tarin daraja a kasuwannin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)