Ghana na tare da yarjejeniyar ta da IMF na magance matsalar tattalin arziƙi

Ghana na tare da yarjejeniyar ta da IMF na magance matsalar tattalin arziƙi

John Dramani  Mahama ya cigaba da cewa ba zai yi watsi da shirin ceto tattalin arzikin ƙasar na dala biliyan 3 dake tsakanin ƙasar da asusun ba da lamuni na duniya IMF ba.

Amma suna kan nazari kan yarjejeniyar da za a shawo kan almubazzaranci da yadda ƙasar ke kashe kudade da kuma inganta fannin makamashi.

Mahama, tsohon shugaban kasar da ya lashe zaben da aka yi a ranar 7 ga watan Disamba, ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters da yammacin, cewa zai yi kokarin shawo kan hauhawar farashin kayayyaki da kuma faduwar darajar kudin kasar, domin dakile matsalar tsadar rayuwa da ya addabi ƙasar da ke yammacin Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)