Ghana na gab da fara tace mai a matatarta mai mafi girma a Afrika

Ghana na gab da fara tace mai a matatarta mai mafi girma a Afrika

Ana sanya ran matatar da za ta kasance karkashin wannan cibiya zata rika tace danyen man fetur akalla ganga dubu dari 9 kowacce rana, matakin da idan ya tabbata zai sanya Ghana gaban kowacce kasa a nahiyar Afrika ta fannin tace mai mafi yawa.

Hukumar da ke sanya idanu kan harkokin man fetur a kasar ta ce ana sanya ran nan da shekarar 2030 za’a samar da matatu guda uku, wadanda dukannin su zasu rika aiki kamar yadda ya kamata.

Kididdiga ta nuna cewa matukar aka cimma wannan buri, gwamnati za ta sami karin kaso 70 cikin 10 na yawan kudaden kasafin kudin da ake bukata da kuma samar da guraben ayyukan yi sama da dubu 800.

Wannan dai wani gagarumin ci gaba ne da kasar wadda ta dogara da shigar da tattaccen man fetur daga ketare ta samu, wanda kuma zai saukakawa ‘yan kasar ta hanyoyi da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)