Adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon kifewar jirgin ruwa a ranar 26 ga Mayu a yankin Wara na jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya ya karu zuwa mutane 92.
Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya sanar da cewa, a aiyukan neman mutanen da jirgin ya kife da su an sake gano jikkunan mutane 16 wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa mtane 92.
Bagudu ya kara da cewa, ana ci gaba da neman mutanen.
A ranar 26 ga Mayu ne jirgin ruwa da ya taso daga jihar Niger ya kife a kogin Wara na karamar hukumar Ngaski da ke jihar Kebbi. Akwai mutane kimanin 160 a cikin jirgin ruwan.