Tun farko dai muhukuntan Mozambique bayyana tserewar fursunoni 1,500 a gidan yarin dake kusa da babban birnin ƙasar Maputo a ranar kirsimeti, sai dai rahotannin baya-bayan nan sun nuna cewa sama da fursuninu dubu 6 ne suka tsere bayan barkewar tarzomar da ya kai ga hallaka mutane 33.
Fursunonin sun yi amfani da tarzomar da ta barke sakamkon zanga-zangar da magoya bayan jam’iyyun adawa ke yi bayan tabbatar da nasarar jam'iyyar Frelimo mai mulki a zaben watan Oktoba.
Shugaban ƴan sandan ƙasar Bernardino Rafael, ya ce fursunoni sun kwace makamai daga hannun masu gadinsu tare sako sauran ƴan uwansu, ciki harda ƴan ta’adda 29 dake zaman wakafi, wanda ya ce abin damuwa ne.
Jami’in ya ce masu zanga-zangar sun yi tattaki har kusa da gidan yarin, tare da lalata motocin ƴan sanda da tashoshi da ababen more rayuwa bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da jam'iyyar Frelimo mai mulki a matsayin wadda ta lashe zaɓen ranar 9 ga Oktoba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI