Wadanda ake zargin sun bayyana ne a gaban wata kotun sojoji da ke a harabar gidan kason Makala a babban birnin ƙasar Kinshasa.
Lauyoyin fursunonin sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ana tuhumar mutanen da suke karewa da laifukan lalata gine gine da haddasa gobara da kuma ayyukan ta’addanci baya ga aikata fyade.
A zaman da ta yi na farko a makon jiya an fuskanci rashin fahimtar juna dangane da laifuka da ake zargin mutanen da aikatawa.
A cikin daren 1 wayewar 2 ga watan satumban nan fursunoni da dama sukayi yunkurin tserewa daga gidan kaso ba tare da yin karin haske game da irin yanayin da lamarin ya afku ba.
Alkalumman wucin gadi da gwamnati ta fitar na cewa akalla mutum 129 suka mutu, 24 daga ciki an harbe su ne da bindiga, gabanin washegari mahukuntan kasar su fitar ƙarin adadin mutun biyu da suka mutu sakamakon raunukan da suka ji.
Ƙungiyar Tarayya Turai, da offishoshin jakadancin Faransa da Belguim dukanin su sun bukaci yin haske game da lamarin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI