Fursunoni 38 sun mika kawunansu ga gwamnati a jihar Imo da ke Najeriya

Fursunoni 38 sun mika kawunansu ga gwamnati a jihar Imo da ke Najeriya

A jihar Imo da ke kudu maso-gabashin Najeriya, fursunoni 38 daga cikin 1,844 da suka tsere daga gidan yari a ranar 5 ga Afrilu sun mika wuya ga jami'an tsaro.

Kakakin Gidan Kurkukun Owerri James Maduba ya shaida cewa, ana ci gaba da aiyukan kamo sauran fursunonin da suka gudu daga gidan yarin sakamakon harin da wasu 'yan bindiga suka kai.

Ministan Harkokin Cikin Gida na Najeriya Rauf Aregbesola ya shaida cewa, fursunonin da suka mika wuya ba za su fuskanci hukuncin guduwar da suka yi ba.

Fursunoni 1,844 ne suka mutu a lokacin da aka kai harin, wasu 35 suka ki guduwa inda aka kuma kona motoci 50.


News Source:   ()