Aƙalla mutane miliyan 6 da dubu 900 alƙaluma suka nuna cewa yanzu haka na fama da matsananciyar yunwar a Somalia sakamakon ƙamfar abinci mai alaƙa da gajeruwar damuna wadda ɗumamar yanayi ta haddasa a ƙasashen yankin ƙuryar gabashin Afrika.
Alƙaluman sun ce wannan adadi na wakiltar duk mutum 2 cikin 5 a ƙasar mai fama da tashe-tashen hankula da ta’addancin ƙungiyar al-Shabaab.
Somalia mai yawan jama’a miliyan 18 da dubu 100 da 4, bayanai sun ce yanzu haka kashi 21 na yawan al’ummar na buƙatar agajin abinci sakamakon matsananciyar yunwar da ta addabesu.
Tun kafin yanzu ne hukumomi irin WFP da hukumar abinci ta majalisar ɗinkin duniya baya ga ƙwararru daga ƙungiyoyi daban-daban ke ta gargadi kan yadda yunwa ka iya addabar ƙasar ta gabashin Afrika inda ko a watan Maris na bara, ƙwararrun suka ce mutane miliyan 26 ka iya faɗawa halin yunwa saboda ƙarancin abincin da ƙasar ke fama da shi.
Baya ga Somalia tarin ƙasashen yankin ne masana suka bayyana cewa za su iya faɗawa wannan matsala ganin yadda sauyin yanayi ya gajarta damunar da suke samu a gefe guda amfani gona da dabbobi ke ci gaba da mutuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI