Fiye da kashi 60 na al’ummar Sudan ta Kudu na cikin barazanar yunwa - MDD

Fiye da kashi 60 na al’ummar Sudan ta Kudu na cikin barazanar yunwa - MDD

Ta cikin wani rahoto da majalisar ta fitar, ta ce a watan Afrilun da ya gabata, kashi 57 na adadin mutanen Sudan ta Kudu sun fuskanci bala’ain yunwa, lamarin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta kwatanta da mai matukar hadari.

Rahoton binciken ya ce adadin mutanen da ake hasashen za su gamu da wannan tashin hankalin ya kai miliyan 7 da dubu dari 7, ƙari kan mutane miliyan 7 da dubu dari 1 da aka samu a bara.

Shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ya koka game da yadda jama’ar Sudan ta Kudu ke basa ɗaukar matakan da suka kamata kan matsalar ta yunwa da rashin abinci mai gina jiki musamman tsakanin ƙananan yara.

Da take bayani shugabar shirin Mary-Ellen McGroarty ta ce lamarin na da ban tsoro, la’akari da ƙarancin abinci da duniya ke fuskanta, abinda ke da alaka ta kai tsaye da tashe-tashen hankula da kuma sauyin yanayi da ake fama da shi.

Sudan ta Kudu na cikin ƙasashe na gaba-gaba da ke fama da tsananin talauci da yunwa mai muni tsakanin jama’arta, baya ga bala’o’I da ke faruwa masu alaka da sauyin yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)