Babban kwamadan ƴan sandan Mozambique Bernardino Rafael wanda ya sanar da lamarin, ya ce fursunonin sun yi amfani da tarzomar bayan zaɓen da ta barke a ƙasar wajen tsarewa.
Jami’in ya ce, kimanin fursononi 1,534 ne suka tsere daga gidan yarin, amma sun yi nasarar sake cafke 150 daga cikinsu.
Fasa gidan yarin na zuwa ne kwana guda bayan mutuwar akalla mutane 21 a tarzomar da ta ɓarke a ranar litinin, bayan da babbar kotun Mozambique ta tabbatar da nasarar ɗan takarar jam'iyyar Frelimo, Daniel Chapo a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar na watan Oktoba mai cike da takaddama.
Matakin da kotun tsarin mulkin ƙasar Mozambique ta ɗauka ya haifar da sabuwar zanga-zanga a faɗin ƙasar, inda magoya bayan jam’iyyun adawa suka fantsama kan tituna saboda zargin da suke yi an tafka maguɗi a zaɓen.
A kalla mutane 78 aka kama ya zuwa yanzu kuma an tsaurara matakan tsaro a faɗin ƙasar, kamar yadda ministan cikin gida Pascoal Ronda ya shaidawa gidan talabijin na TVM a ranar Talata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI