Firaministan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Firmin Ngrebada ya mika takardar yin murabus ga Shugaban Kasar Faustin Archange Touadera.
Sanarwar da Ngrebada ya fitar ta shafin Twitter ta bayyana cewa, ya mikawa Shugaba Youadera takardar murabus tare da majalisar ministocinsa.
Tun shekarar 2019 Ngrebada yake a kan kujerar Firaministan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Ana sa ran nan da kankanin lokaci Shugaba Touadera zai sanar da sabuwar majalisar zartarwa.