Firaministan Ivory Coast Amadou Gon Coulibaly ya kwanta dama.
Labaran da jaridun kasar suka fitar na cewa a yayin zaman Majalisar Zartarwa a ranar Larabar nan ne Coulibaly ya sanar da ba ya jin dadi, kuma a watan Mayu ya je Faransa don a duba lafiyar zuciyarsa inda ya dawo kasarsa a ranar 2 ga watan Yuli.
An kai Coulibaly wani karamin asibiti mai zaman kansa a Abidjan Babban Birnin Kasar inda duk kokarin ceton ransa da aka yi ya ci tura.
Coulibaly da yake dan takarar jam'iyyarsa a zaben Shugaban Kasar da za a yi a ranar 30 ga watan Oktoba, a watan Maris ya yi mu'amala da wani mai dauke da cutar Corona, amma bayan yi masa gwaji sau 2 aka bayyana ba ya dauke da cutar.
A watan Mayu Coulibaly mai shekaru 61 ya je Faransa don duba lafiyarsa inda aka bayyana masa cewar an samu wani datti a zuciyarsa, kuma likitoci suka bukaci da ya kwanta don ya huta.