Firaministan Aljeriya ya gabatar da wasikar murabus dinsa

Firaministan Aljeriya ya gabatar da wasikar murabus dinsa

Firaministan Aljeriya, Abdelaziz Djerad ya gabatar da takardar murabus dinsa ga Shugaba Abdelmadjiid Tebboune bayan da aka sanar da sakamakon babban zaben da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yuni a hukumance.

A cikin sanarwar da Fadar Shugaban kasar ta fitar, an bayyana cewa Tebboune ya tarbi Firaminista Djerad a Ofishin Shugaban kasa da ke babban birnin kasar.

A cikin sanarwar, an bayyana cewa Djerad ya gabatar da wasikar murabus dinsa ga shugaban kasar bayan da aka sanar da sakamakon zaben a hukumance.

An kuma bayyana cewa an amince da murabus din Djerad, amma zai ci gaba da aikinsa har zuwa lokacin da za a kafa sabuwar gwamnatin.

An bayar da rahoton cewa Tebboune ya gode wa Djerad saboda nasarar da ya samu na gudanar da aikinsa a cikin mawuyacin lokacin annobar sabon nau'in kwayar cutar corona (Covid-19).

Dangane da sakamakon zaben gama gari da aka gudanar a Aljeriya a ranar 12 ga watan Yuni, Jam’iyyar UKC ta zama jam’iyya ta farko da ke da kujeru 98. A Majalisar Wakilai mai kujeru 407, masu cin gashin kansu sun samu kujeru 84, masu ra'ayin musulinci na Jam’iyyar Zaman Lafiya 65, Jam’iyyar RND 58, Jam’iyyar Gaba 48, Jam’iyyar Gina Kasa 39 da kuma Jam’iyyar Adalci da Ci gaba da suka ci kujeru 2.


News Source:   ()