Ta cikin jawabin da ya yi a kafafen yaɗa labaran ƙasar Felix Tchikedi ya ce gwamnati nada ƙwararan jawabai da ke nuna cewa Joseph Kabila na haɗa wata tawaga don tayarwa da gwamnati ƙayar baya.
Tchikedi ya kuma ci gaba da cewa Kabila ne ke jagorantar kungiyar ƴan tawaye ta Alliance Fleuve Congo.
Ƙungiyar tawayen ta AFC na cikin ƙungiyoyin da ke riƙe da makamai da sunan juyin juya halin siyasa da kuma taimakawa ƙungiyoyin ta’addanci irin su M23 da sauransu a cewar sa.
A watan Disamban bara ne Corneille Nangaa tsohon shugaban hukumar zaɓen ƙasar ya sanar da kafa ƙungiyar AFC da sunan siyasa, sai dai a yanzu ana zargin ta juye zuwa ƙungiyar tawaye.
Kabila ya riƙe shugabancin ƙasar a shekarar 2001 bayan kashe mahaifinsa Laurent-Desire Kabila wanda shi kuma yayi wa wanda ya gada Mobutu Sese Seko juyin mulki a 1997.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI