Faye ya ƙaddamar da shiri mai dogon zango dan ciyar da Senegal gaba

Faye ya ƙaddamar da shiri mai dogon zango dan ciyar da Senegal gaba

Sai dai gwamnatin Senegal ɗin ta bayyana wasu daga cikin muradun da tsara cim-musu cikin shekaru 5.

Muhimman muradun da take fatan cim-musu a gejeren zango kuwa, sun haɗa da rage nauyin bashin da ke kan ƙasar daga kaso 83.7 zuwa kaso 70 cikin 100.

Sai kuma rage giɓin kasafin kuɗi zuwa kashi 3 nan gaba kaɗan, saɓanin giɓin kashi 10.4 da ƙididdiga ta nuna cewar gwa,natin senegal din ta yi fama da shi daga shekarar 2019 zuwa 2023.

Ƙalubale na gaba da gwamnatin Senegal ta sha alwashin magancewa shi ne matsin rayuwa, inda ta yi alƙawarin cikin shekaru biyar da ke tafe, za ta ƙara yawan matsakaicin albashin da ‘yan ƙasar ke samu da kashi 50 cikin 100, kwatankwacin ƙarin daga dala dubu 1, 660 zuwa aƙalla dala dubu 2,648, yayin da kuma za a rage hauhawar farashin kayayyaki zuwa kashi 2 cikin shekaru 5.

Shugaban Senegal Basirou Diomaye Faye da Fira Ministansa Ousmane Sonko ne suka jagoranci kaddamar da gagarumin shirin a garin Diamniadio, mai nisan kilomita 30 daga Dakar babban birnin ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)