Gwamnan Lardin Kudancin Kivu da ke gabashin Jamhuriyar Congon Jean Jacques ne ya tabbatar da adadin mamatan na mutane 78, da kuma yawan fasinjojin kusan 300 da ke cikin jirgin da ya nutse.
Sai dai ya ce basu kammala tantance adadin rayukan da suka salwanta a haɗarin ba, aikin da ya ce zai ɗauki jami’an ceto aƙalla kwanaki uku suna yi.
Har zuwa daren jiya dai an riƙa samun bayanai masu cin karo da juna akan yawan waɗanda haɗarin jirgin ruwan ya rutsa da su, domin a yayin da mahukuntan lardin Kivu suka bayar da nasu alƙaluman, takwarorinsu na arewacin Lardin Kivun cewa suka yi mutane 28 suka rasa rayukansu, yayin da wasu 58 suka tsira.
Ɗaukar fasinjoji fiye da kima ke kan gaba a cikin dalilan dake haddasa yawaitar nutsewar jiragen ruwa a Jamhuriyar Congo, lamarin da ake kyautata zaton ko a wannan karon shi ne musababbin haɗarin da ya auku.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI