Ƙungiyar raya ƙasashen yankin kudancin Afrika SADC da ke wakiltar ƙasashe 16 yayin babban taronta a Harare ta bayyana babban ƙalubalen ƙarancin abincin da ke tunƙaro yankin a matsayin lamarin da ke tagayya tattalin arziki yankin da kuma ta’azzarar buƙatar neman ɗaukin ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa.
Tun a farkon shekarar 2024 ne yankin na kudancin Afrika ya fara fuskantar fari sakamakon bushewar amfani gona da kuma mutuwar tarin dabbobi na ruwa da na ban ƙasa lamarin da ya tsanantar matsalar ƙarancin abinci tare da haddasa babbar illa ga tattalin arziƙin yankin.
Babban sakataren ƙungiyar ta SADC Elias Magosi ya bayyana cewa mutane miliyan 68 da ke wakiltar kashi 17 na yawan al’ummar ƙasashen yanzu haka na tsananin buƙatar agaji.
Yanayin zubar ruwan saman da yankin na kudancin Afrika ya fuskanta a bana ya sha banban da yadda aka saba ganin damuna wanda ke zuwa bayan gargaɗin masana da ke bayyana yiwuwar fuskantar ƙarancin abinci a yankin.
Sauyin yanayi da tsananin zafi da ke tafarfasa teku ya shafi ƙasashen Zimbabwe da Zambia da Malawi waɗanda tuni suka ayyana dokar ta ɓaci kan yunwa yayinda Lesotho da Namibia suka fara kiraye-kirayen neman agajin ƙasashe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI