An bayyana cewa dubun dubatan mutane zasu tilastu da yin hijira daga kasar Somaliya sabili da fari da dumaman yanayi.
Daraktan Hukumar Ýan Gudun Hijira na kasar Norway Muhammad Abdi ya bayyana cewa Somaliya na fuskantar matsanancin fari.
Ya kara da cewa sabili da rashin ruwa da mazauna wasu yankunan kasashe zasu sha su shayar da dabbobinsu zasu tilastu da kauracewa yankunansu zuwa yankunan dake da ruwa.
Abdi ya jaddada cewa yankunan Somaliya 50 na fuskantar matsalar rashin ruwa kuma yanayin na cigaba da gurbata.
A shekarar bara Somaliya fiye da miliyan daya suka kauracewa gidajensu sabili da rashin ruwa da fari.
A cikin watanni ukun farkon shekarar bana mutane dubu 112 sun yi kaura daga matsugunansu.