Fargabar juyin mulki ta tilastawa Salva Kiir dakatar da balaguro zuwa ƙetare

Fargabar juyin mulki ta tilastawa Salva Kiir dakatar da balaguro zuwa ƙetare

Duk da rashin lafiyar da shugaban na Sudan ta kudu ke fama da shi wanda likitoci suka nemi ya fita ƙetare don duba lafiyarsa, halin da ƙasar ta shiga ya tilasta shugaban dakatarwa tare da kiran taron gaggawa na majalisar ministocinsa da kuma ɓangarorin tsaron ƙasar mai fama da rikici.

Kwana guda bayana musayar da aka fuskanta a gidan tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar ta Sudan ta kudu Akool Koor ne cikin gaggawa shugaba Kiir ya kira taron, bayan fitar wasu bayanai da ke nuna yiwuwar a iya yi masa juyin mulki.

Tun kafin musayar wutar ta gidan Akool Koor dama akwai jita-jitar juyin mulki a ƙasar wadda ke ganin mummunar koma baya sakamakon tarin rikice-rikice masu alaƙa da ƙabilanci.

Mahukuntan na Juba sun tuhumi Koor da hannu a yunƙurin kifar da gwamnatin Kiir wanda ya kai ga korar shi daga bakin aiki tun a baya, gabanin ɗaure shi a yanzu bayan musayar wutar da ta faru a gidansa cikin makon jiya.

Zaman tankiya tsakanin bangarori masu rikici da juna ya ci gaba da tsananta a Sudan ta kudu musamman bayan matakin gwamnati na sake ɗage zaɓen ƙasar wanda ya sanya fargabar yiwuwar ɓarkewar rikici.

Rahotanni sun ce Kiir ya kira taron ne don kaucewa duk wata barazana da ka iya tasowa bayan da ya yi umarnin kame Akol Koor mai ɗimbin magoya baya galibi a cikin hukumomin tsaron ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)