Ƴan tawayen Azbinawa dai sun zargi sojojin Mali da dakarun Wagner da kai harin da aka kai yankin Tinzaouatene na kusa da Algeria, inda su ka ce adadin waɗnda suka mutu ya kai 21, cikin su yara ƙanana 11.
A yankin Tinzaouatene ne aka gwabza faɗa tsakanin ƴan tawaye da dakarun gwamnati a watan Yuli, arangamar da ƴan tawaayen Azbinawan suka ce sun samu galaba a kan sojoin Mali da dakarun Wagner.
Kakin ƴan tawayen, Elmaouloud Ramadane ya ce tun da farko wani shagon sayar da magunguna ne aka fara kai wa harin, kafin daga bisani aka kai farmaki kan taron jama’a, a kusa da inda aka kai harin farko.
Tun da ta karɓe iko a shekarar 2020, gwamnatin ssojin Mali ta bai wa batun sake ƙwace yankunanta daga hannun ƴan tawaye da mayaka masu ikirarin jihadi masu alaƙada Al-Qaeda mahimmanci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI