Wasu mazauna lardin Gnagna inda lamarin ya faru ssun ce ƴan ta’addan sun farmaki garin ne da yammacin Lahadi, inda su ka kashe mutane tare da raunata da dama.
Wani jami’in asibiti a yankin ya ce yana da matuƙar wahala a tantance adadin waɗanda su ka mutu, amma ya ce akalla mutane 10 sun mutu, kana 50 su ka jikkata.
Ganau sun ce maharan sun sun shiga garin ne kuma su ka fara harbi kan uwa da wabi, inda su ka tarwatsa jama’a, har su ka fara fasa shaguna su na sata.
Ƙasar da ke yankin yammacin nahiyar Afrika tana fama da matsalar ƴan ta’adda masu ikirarin jihadi da su ka kwarara daga makwafciyarta Mali tun daga shekarar 2015.
Dubban fararen hula, sojoji da yan sanda ne aka kashe, lamarin da ya fusata wasu hafsoshin soji har su ka yi juyin mulki a shekarar 2022.
Sama da mutane dubu 26 ne su ka mutu sakamakon hare-haren ƴan ta’adda a Burkina Faso tun daga shekarar 2015, fiye da dubu 6 daga cikin su a wannan shekarar aka kashe su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI