Fararen fatar Afirka ta Kudu tayi watsi da buƙatar Shugaban Amurka

Fararen fatar Afirka ta Kudu tayi watsi da buƙatar Shugaban Amurka

Shagaban na Amurka Donald Trump  ya bayyana wannan bukatar tasa ce a yayin da ya rattaɓa hanu akan wani umarni nasa da ya katse tallafi da ƙasarsa ke baiwa Afirka

Yace ya katse tallafin ne sakamakon wata dokar da shugaban ƙasar Cyril Ramaphosa ya rattaɓawa hanu, kan gyara tsarin amfani da filaye na ƙasar domin kawar da bambance-bambancen da aka samu a sanadiyar ƙarfin ikon farar fata a ƙasar a baya.

Wannan umarnin ya samar da yadda za a sake tsugunar da Amurkawa dake Afirka ta kudu a Amurka da suka fuskanci matsalar wariyar a ƙasar.

Sai dai dokar da Ramaphosa ya rattaɓawa hanu na shirin magance matsalar wariyar akan mallakar filaye a yayin da farar fata marasa rinjaye suka mallaki mafi akasarin adadi na filaye a ƙasar, domin sauƙaƙa yadda harkar filaye zata yi tasiri yadda ta dace.

Farar fata dai a ƙasar ta Afirka ta kudu sune da kashi 7.2% na al’umar ƙasar mai yawan mutane miliyan 63 kamar yadda hukumar ƙididdigar ƙasar ta bayyana.

Jam’iyar shugaba Ramaphosa ta ANC itace mafi girma a ƙasar, wadda tace shugaban na Amurka na amfani da wasu bayanai ne marasa tushe balle makama, da wata ƙungiyar farar fatar ƙasar Afriforum ke ta farfaganda dasu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)