A lokacin da Macron ke gabatar da jawabi a zauren majalisar dokokin ƙasar a ziyarar kwanaki uku da yakai ƙasar, ya ce kamfanonin Faransa za su goyi bayan gina yankin, wanda makomarshi ke ƙarkashin ikon Morocco.
Wannan dai na zuwa ne bayan da ƙasashen biyu suka cimma yarjejeniyar samada euro biliyan 10, a ɓangaren gine-gine da makamashi.
Duk da cewa babu ƙarin bayani game da yarjejeniyar da aka cimma, amma dai kamfanin gina layin dogo na Faransa Alstom, zai kai kashi 18 na jiragen ƙasa da ake buƙata a Morocco.
Macron ya kai ziyara Morocco ne sakamakon gayyatar da Sarki Mohammed ya yi masa a ƙarshen watan Satumbar daya gabata, bayan da ruwa ya yi tsami tsakani a tsakaninsu cikin tsawon shekaru.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI