Umurnin zai soma aiki ne daga wanan watan na Octoba inda aka bukaci Shugaban tsibirin mayotte dake karkashin ikon Faransa ya tsara ruku-rukunin jirage domin jigilar baki ‘yan asalin Jamhuriya Dimokradiyar Congo da basu mallaki takardu ba zuwa gida.
Wata majiya ta kusa da ministan cikin gidan Faransa ta Fadawa kamfanin dillancin labaran AFP cewa, tun cikin watan fabarairun da ya wuce akayi tanadin jirage 4 da zasu yi aikin tareda yawun gwamnatin Jamhuriya Dimokradiyar Congo.
Tun daga karshen shekara 2010 aka fara samun kwarara daruruwan bakin haure ‘yan Afirka mafi aksarin su daga Jamhuriya Dimokradiyar Congo wadanda ke tsallakawa kowace shekara cikin tsibirin ta barauniya hanya.
Alkalumman hukuma sun ce fiye da rabin al’umma tsibirin Mayotte da suka tasa dubu 320 ,basu mallaki takardun zama ‘yan kasa ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI