Shugaban ya bayyana hakan ne ranar Jumma’a gaban sojojin Faransa kimanin 1500 da ke sansanin sojin saman ƙasar dake Djibouti, inda ya je bukin kirsimeti kamar yadda ya saba ziyarar sojojin Faransa a ƙasashen Afirka a duk shekara.
Tuni dai aka tilastawa Faransa ta kwashe sojojinta daga Mali da Burkina Faso da Nijar a tsakanin shekarar 2022 zuwa 2023 bayan da sojoji suka hau karagar mulki tare da kulla alaka da Rasha.
Chadi
A halin da ake ciki ma, tawagar farko na sojojin Faransa 120 su ma sun bar ƙasar Chadi a ranar Juma’a 20 ga watan Disamba, kamar yadda rundunar sojin Chadi ta sanar ta shafin Facebook.
A ranar 29 ga watan Nuwamba Chadi ta sanar da kawo ƙarshen yarjejeniyar tsaro tsakaninta da Faransa, in ta bukaci ta gaggauta janye dakarunta daga ƙasar kafin ranar 31 ga watan Janairu.
Ƙasar Senegal ma ta bi sahun kasashen na Sahel wajen bayyana fatar ganin Faransa ta rufe sansanonin sojinta dake ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI