Faransa za ta janye sojojinta daga Cote d'Ivoire - Alassane Ouattara

Faransa za ta janye sojojinta daga Cote d'Ivoire - Alassane Ouattara

Da yake jawabin ƙarshen shekara ga al'ummar ƙasar, ranar Talata Ouattara ya ce Faransa za ta mika sansanin sojinta da ke Abidjan ga sojojin ƙasar a hukumance cikin kwanaki masu zuwa.

Za mu yi alfahari da sojojin mu wanda zamani ya yi tasiri a yanzu. A cikin wannan tsarin ne muka yanke shawara kan shirin janyewar sojojin Faransa a Cote d'Ivoire

Faransa wacce mulkin mallaka da ta yi a yammacin Afirka ya kawo ƙarshe a shekarun 1960, tuni ta janye sojojinta daga Mali da Burkina Faso da Nijar, bayan da sojoji da suka yi juyin mulkin a kasashen suka raba gari da ita tare da nuna mata kyama.

Gwamnatin ƙasar Chadi ma, ba zato ba tsammani ta kawo ƙarshen yarjejeniyar hadin gwiwa ta tsaro dake tsakanita da Faransa a watan Nuwamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)