Firaministan Faransa Gabriel Attal da ke shirin barin kujerar mulki da kansa ne ya sanar da shirin tallafa wa ƙasashen na Afrika da rigakafin cutar ta Ƙyandar Birin musamman ga yankunan da aka fi ganin ta’azzarar cutar, a wani yanayi da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ke cewa karon farko tun bayan fara ganin tsanantar cutar a shekarar 2022, Ivory Coast ta sanar da samun masu ɗauke da cutar.
Mahukuntan Ivory Coast sun ce sun samu mutane biyu da ke ɗauke da nau’in cutar ta ƙyandar, lamarin da ya sanya mahukuntan ƙasar tsaurara matakan gwaji baya ga laluben rigakafin yaƙi da cutar.
Cikin saƙon da Attal ya wallafa a shafinsa na X ya bayyana cewa a mako mai kamawa ne Faransa za ta miƙa alluran rigakafin ta hannun ƙungiyar EU ga Afrika dai dai lokacin da Amurka ke shirin baiwa nahiyar wasu ƙarin alluran cutar dubu 50 don daƙile yaɗuwarta.
A makon jiya ne hukumar lafiyar ƙungiyar tarayyar Afrika ta ce za a samar da alluran rigakafi dubu 200 ga nahiyar ƙarƙashin yarjejeniyar da nahiyar ta ƙulla ƙungiyar EU da kuma kamfanin harhaɗa magunguna na Denmark.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI