Faransa ta yi tir da hare-haren da mayaƙan M23 ke kaiwa yankin Goma

Faransa ta yi tir da hare-haren da mayaƙan M23 ke kaiwa yankin Goma

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot ne ya bayyana haka a lokacin da ya isa majalisar ministocin ƙungiyar Tarayyar Turai da ke birnin Brussels, inda ya ce lokaci ya yi da ya kamata a kawo ƙarshen rikicin ta hanyar komawa kan teburin tattaunawa.

Faransa na Allah wadai da hare-haren da mayaƙan M23 da ke samun goyon bayan Rwanda ke kaiwa wanda ya yi sanadiyar mutuwar jami’an da ke aikin wanzar da zaman lafiya 6, tare da raba daruruwa da muhallansu.

Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo ta yanke hulɗar jakadanci da Rwanda, ya yin da kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya kira taron gaggawa don tattauna batun rikicin.

A cikin ƴan makwannin nan dai rikici ya sake kazancewa a yankin na Goma, inda ko a jiya Lahadi sai da ƴan tawayen na M23 suka yi ikirarin kwace ikon birnin daga hannun dakarun ƙasar.

Tuni dai ƙasashen Amurka da Birtaniya da Faransa suka umarci al’ummarsu da ke zaune a yankin Goma su gaggauta ficewa daga cikinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)