Faransa ta taka babbar rawa a kisan kiyashin Ruwanda

Faransa ta taka babbar rawa a kisan kiyashin Ruwanda

Faransa ta taka gagarumar rawa a kisan kare dangi da aka yi a Ruwanda, kuma gwamnatin lokacin ta gano yiwuwar kisan kiyashin zai afku.

An mikawa gwamnatin Kigali wani rahoton bincike mai shafuka 600 da gwamnatin Ruwanda ta dauki nauyin wani kamfanin lauyoyi na Amurka mai suna "Levy Firestone Muse" don gudnarwa, wanda ya a shekarar 2017 ya fara gudanar da binciken mai taken "Hasashen kisan kiyashi: Rawan da Faransa ta taka wajen kisan kiyashi ga Tutsi a Ruwanda".

Rahoton ya bayyana cewa, Faransa ta hada kai da gwamnatin Hutu wajen kashe al'umar Tutsi dubu 800,an kuma yi watsi da cewar wai gwamnatin Paris ba ta da labarin gwamatin Hutu za ta aikata kisan kiyashin.

Rahoton ya kara da cewa, "Gwamnatin Faransa tana da labarin za a yi kisan kiyashin, kuma ta san da shi."

Haka zalika rahoton ya ci gaba da cewa, Faransa ta san za a yi kisan kiyashin, kuma ba ta yi sanya ba wajen bayar da goyon baya ga abokanta na Ruwanda.

Rahoton ya ce, "Mun samu cikakken sakamakon da ke nuna Faransa ta san za a yi kisan kiyashin, ta taka muhimmiyar rawa wajen kisan kare dangin."

An yi nazari kan miliyoyin takardu da sauraren shaidu sama da 250, inda ba a samu shaida da ke nuna shugabannin Faransa sun sanya hannu kai tsaye ba wajen kisan jama'ar Tutsi.

A shekarar 1994 ne aka fara kisan kiyashi ga jama'ar Tutsi a Ruwanda bayan da al'umar Hutu suka zargi Tutsi da harbo jirgin saman Shugaban Kasar Juvenal Habyarimana.

A rikicin da aka yi na kwanaki 100 a kasar an kashe jama'ar Tutsi sama da dubu 800.


News Source:   ()