Faransa ta mika wa Chadi sansanin sojinta na karshe da ke kasar

Faransa ta mika wa Chadi sansanin sojinta na karshe da ke kasar

Ko da yake Chadi ce ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar tsaro, shugaban rundunar sojojin Faransa a Afirka ya bayyana cewa matakin wani bangare ne na shawarar Faransa.

Shugaban rundunar sojojin Faransa a Afirka, Pascal Ianni ya ce, fivewar dakarun na daga cikin shawarwarin Faransa na kawo karshen sansanonin soji da ta kafa a Yammaci da kuma Tsakiyar Afirka.

Wannan dai na zuwa ne, bayan da Faransa ta mika wasu sansanonin sojinta biyu ga gwamnatin Chadi.

Bayanai sun jiyo, babban hafsan hafsoshin sojojin Chadi, Abakar Abdelkerim Daoud, na yabawa da shawarar kawo karshen huldar tsaro tsakanin Faransa da kasarsa, tare da cewa sojojin Chadi na da karfin aikin da sojojin Faransa ke takawa a kasar.

 Kafin karshen yarjejeniyar, Faransa na da kusan dakaru 1,000 da ta jibge a kasar Chad, domin aikin wanzar da zaman lafiyai.

Bayan fafatawa da masu tayar da kayar baya da sojojin yankin Sahel, Mali, Nijar da Burkina Faso sun bukaci ficewar sojojin Faransa daga kasashensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)