Faransa ta mayar da tsoffin kayan tarihi zuwa kasar Habasha

Faransa ta mayar da tsoffin kayan tarihi zuwa kasar Habasha

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot ya mika gatari guda biyu na dutse da aka yi kafin tarihi, wadanda ake kira bifaces, da kuma na sassaka dutse ga ministar yawon bude ido ta Habasha Selamawit Kassa, a ziyarar da ta kai a gidan tarihi na kasa da ke Addis Ababa.

 Kayayyakin sun kasance "samfuran kayan tarihi kusan 3,500 daga tonon sililin da aka gudanar a wurin Melka Kunture", wani gungu na wuraren tarihi a kudancin babban birnin kasar da aka tono karkashin jagorancin wani mai bincike na Faransa, Barrot.

 Faransa da Habasha sun kulla yarjejeniya mai dadadden tarihi kan yin hadin gwiwa a fannonin ilmin kimiya na kayan tarihi da burbushin halittu.

Kayayyakin tarihi da a halin yanzu ake ajiye su a ofishin jakadancin Faransa da ke Addis Ababa, za a kai su gaba daya ga hukumar kula da kayayyakin tarihi ta Habasha ranar Talata.

Mai ba da shawara kan al'adu a ofishin jakadancin Faransa, Laurent Serrano, ya shaida wa AFP cewa, "Wannan mika hannu ne, ba fansa ba, domin abubuwan ba su taba kasancewa cikin tarin jama'a na Faransa ba." Ya kara da cewa, "wadannan kayayyakin tarihi, wadanda aka samo su a tsakanin shekaru miliyan 1 zuwa 2, an same su ne a lokacin da aka tona akayan tarihi da aka shafe shekaru da dama ana yi a wani wuri kusa da babban birnin kasar Habasha."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)