An tabbatar da an kashe fararen hula 19 a ranar 3 ga Watan Janairu sakamakon wani hari da aka kai ta sama a Mali a karkashin Farmakan Barkhane.
Labaran da jaridun Faransa suka fitar na cewa, Ofishn Kula da Dakarun Majalisar Dinkin Duniya Masu Wanzar da Zaman Lafiya a Mali ya kammala binciken da ya fara game da zargin kashe fararen hular.
Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, a karkashin Farmakan Barkhane an kashe fararen hula 19 a yayinda aka kai hari ta sama a yankin Bounti.
Rahton ya nuni da cewa, an kai harin kan jama'a kusan 100 da ke taron aure, kuma an bayyana kashe 'yan ta'addar Alka'eda 3 wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa 22.