Faransa da Morocco sun ƙulla yarjejeniyar sama da euro biliyan goma

Faransa da Morocco sun ƙulla yarjejeniyar sama da euro biliyan goma

Wata majiya da ke da masaniya kan yarjejeniyar, ta shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, an cimma yarjejeniyar ce a ɓangaren makamashi da gine-gine da aka sanyawa hannu a gaban shugabanin ƙasashen biyu.

Duk da cewa babu ƙarin bayani game da yarjejeniyar da aka cimma, amma dai kamfanin gina layin dogo na Faransa Alstom, zai kai kashi 18 na jiragen ƙasa da ake buƙata a Morocco.

Haka nan ana saran a wannan rana ta Talata, za a ƙara cimma wasu yarjeniyoyi tsakanin ƙasashen biyu. 

Macron ya kai ziyara Morocco ne sakamakon gayyatar da Sarki Mohammed ya yi masa a ƙarshen watan Satumbar daya gabata, bayan da ruwa ya yi tsami tsakani a tsakaninsu cikin tsawon shekaru.

Tawagar da ta yiwa Macron rakiya zuwa Morocco ta ƙunshi ministan harkokin cikin gidan ƙasar Bruno Retailleau da na tattalin arziki Antoine Armand da kuma ta al’adu Rachida Dati wacce ke da tsatson Marocco.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)