EU ta miƙawa Ghana tallafin Yuro miliyan 50 domin inganta bangaren tsaro

EU ta miƙawa Ghana tallafin Yuro miliyan 50 domin inganta bangaren tsaro

A shekarun baya-bayan nan dai harkokin tsaro suka taɓarɓare a yankin, inda ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi wadanda ke da alaka da Al-Qaeda da kungiyar IS ke barazanar faɗaɗa ayyukansu daga yankin Sahel zuwa kasashen da ke gabar teku kamar Ghana, Ivory Coast da Benin.

Tallafin na EU dai ya biyo bayan tallafin motocin sulke guda 105 da ta miƙa wa ƙasar a shekarar 2023, bayan wata yarjejeniya da suka cimma ta tallafin tsaro, wadda za ta kai har zuwa shekarar 2026.

Ministan tsaron ƙasar ta Ghana, Edward Omane Boamah ya ce kayan aikin da EU ta bai wa Ghana, zai ba wa jami’an tsaro ƙarfin gwiwar kare ‘yan ƙasar daga barazanar masu ɗauke da makamai, da kuma kare martabar dimokraɗiyya.

Shi ma dai jakadan Tarayyar Turai a Ghana, Irchad Razaaly ya ce Ghana da ƙungiyar za su ci gaba da yin aiki tare, wajen tunkarar matsalolin tsaro da kuma fasaƙwauri.

Tallafin na EU ya yi daidai da yunƙurin ƙasashen duniya, na shawo kan matsalar rashin tsaro a yankin Sahel da kuma ƙarfafa rawar da Ghana ta taka wajen yaƙi da rashin zaman lafiya a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)