Ethiopia da Somalia sun fara yunkurin kawo ƙarshen takun sakar da ke tsakaninsu

Ethiopia da Somalia sun fara yunkurin kawo ƙarshen takun sakar da ke tsakaninsu

Ganawar dai ta guna ne tsakanin ƙaramin ministan harkokin wajen Somalia Ali Mohamed Omar da takwaransa na Habasha Mesganu Arega, bayan da dakarunsu suka fafata a Jubaland da ke iyakar Somalia a ranar litinin.

Wasu majiyoyi daga Jubaland sun ce sojojin gwamnatin Somalia a makonnin baya-bayan nan suna kai hare-hare yankin, yayin da sojojin Habasha ke samar da kariya ga wasu ƴan siyasar yankin daga hare-haren da ake kai musu a garin Doolow.

To sai dai ƙasashen biyu a jiya Talata sun nuna sha'awar farfaɗo da alaƙarsu don ci gaba da hulɗarsu ta baya, bayan da Turkiyya ta shiga tsakani don daidaita su.

Tun a watan Janairun wannan shekarar ne dai ƙasashen biyu ke takun saka da juna, bayan Habasha ta kulla yarjejeniya da yankin Somaliland da ke ƙoƙarin ɓallewa daga Somalia, yarjejeniyar da ta amince Habasha ta samar da tashar ruwa da sansanin soji a wani ɓangare na yankin, sannan ita kuma ta amince da ƴancin kan yankin, ko da yake ko sau ɗaya Addis Ababa ba ta taɓa furta hakan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)