Eritrea ce kawai kasa a Afirka da ba ta fara allurar riga-kafin Covid-19 ba

Eritrea ce kawai kasa a Afirka da ba ta fara allurar riga-kafin Covid-19 ba

A wani bangare na yakar sabon nau'in kwayar cutar corona (Covid-19), an ba da rahoton cewa Eritrea ita ce kawai ƙasa a cikin nahiyar Afirka da har yanzu ba ta fara yin allurar riga-kafi ba.

Bayan da aka fara kamfen din allurar riga-kafin cutar a Tanzaniya a ranar 28 ga Yuli kuma Burundi ta sanar da cewa ita ma za ta fara yin allurar, Eritrea ta kasance kasa daya tilo a nahiyar da ba a fara yin allurar riga-kafin Covid-19 ba.

A halin da ake ciki, kashi 1.6 cikin dari na yawan mutanen nahiyar ne suka samu cikakkiyar riga-kafin cutar, a cewar ofishin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a Afirka.

Rahoton ya ce, a nahiyar Afirka, Seychelles ta yi allurar riga-kafin ga fiye da kashi 68 cikin 100 na al'ummarta, yayin da Mauritius ita ce kasar da aka fi samun yawan allurar riga-kafin da kashi 33 cikin dari da Marokko mai kashi 26 cikin dari.

A Eritrea mutane 35 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar ya zuwa yanzu, sannan an tabbatar da cewa mutane dubu 6 da 547 sun kamu da cutar.


News Source:   ()