
Kamfanin dillancin labarai na Turkiya Anadolu ne ya ruwaito shugaba Recep Tayyib Erdogan na miƙa tayin na shiga tsakanin yayin wata ganawarsa da shugaba Paul Kagame na Rwanda a yammacin jiya Alhamis.
Erdogan ya ce a matsayinsu na Turkiya a shirye suke suyi dukkan mai yiwuwa wajen ganin ta samar da fahimtar juna tsakanin ƙasashen biyu maƙwabtan juna wanda shi ne zai haifar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin na gabashin Afrika.
Kalaman na Erdogan na zuwa a wani yanayi da ƴan tawayen M23 masu samun goyon bayan Rwanda ke ci gaba da ƙwace yankuna masu muhimmanci a cikin Congo, lamarin da ya bayyana raunin da dakarun na Kinshasa ke da shi a fagen daga.
Ko a farkon watan nan mutane fiye dubu 230 suka tsere daga matsugunansu bayan da ƴan tawayen na M23 suka yi kawanya ga Goma, birni mafi girma a lardin arewacin Kivu, a gefe guda Majalisar ɗinkin duniya ke cewa rikicin ka iya juyewa zuwa na yanki baki ɗaya sabanin tsakanin kasashen biyu.
Akwai zarge-zargen da ke nuna cewa hatta Sojin Rwanda yanzu haka na a cikin ƙasar ta Congo inda suke fatattakar Sojojin na Kinshasa sai dai duk da haka Erdogan ya ce yana da yaƙinin rikicin zai warwaru ta fuskar diflomasiyya.
Kafin yanzu, Erdogan ya kuma shiga tsakani a rikicin Somalia da Habasha inda tuni suka hau teburin sulhu bisa jagorancin Ankara, lamarin da ake kallo a matsayin yunƙuri ƙasar mai sassa a nahiyoyi 3 na ganin ta karfafa manufofinta kama daga Diflomasiyya da kuma tattalin arziki a Afrika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI