Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya tattauna da Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ta wayar tarho.
A yayin tattaunawar, Erdogan da yake bayyana cewa suna kokarin ba da darasin da ya kamata ga kasashen duniya, ya ce "Isra'ila ba ta da doka, adalci da lamiri" saboda hare-haren da take kaiwa Falasdinu.
A yayin ganawar inda aka kuma kimanta alakar kasashen biyu da ci gaban yankunan, Erdogan ya bayyana cewa ya yi imanin cewa Najeriya za ta nuna hadin kai ga Falasdinawa a kan dalilin ta na gaskiya.
Shugaba Erdogan da Shugaba Buhari sun kuma taya juna murnar bukin karamar Sallah yayin taron.