Gwamnatin ta ce ta ɗauki wannan mataki ne ta hanyar haɗa kai da kamfanin whatsapp wajen daƙile sauke duk wani fai-fan bidiyo.
Baya ga wannan kuma, gwamnatin ta sha alwashin sanya kyamarorin nadar bayanan sirri a ofisoshin gwamnati.
An dai sami faya-fayan bidiyon lalata da matan fitattun mutane na ƙasar sama da 400 a ofishin shugaban hukumar wata, Baltasar Engonga, tun daga nan ne kuma ƙasar ta shiga cikin ruɗani.
Bayanai sun ce tuni aka fara samun matan da ke hallaka kansu a sakamakon fitar wannan asiri.
Tun farko dai an zargi Baltasar da laifin cin hanci da rashawa, dalili kenan da ya sa aka yanke hukuncin binciken ofishinsa kuma nan take aka gano waɗannan faya-fayan bidiyon.
Cikin matan da aka samu ya aikata lalata da su, sun haɗar da matar ɗan uwansa, da wasu daga cikin ƴan uwansa, uwargidan babban sufeton ƴan sandan ƙasar da kuma matan ministoci akalla 20 da sauran matan manyan mutane.
Tun bayan fitar faya-fayan bidiyon ne ƴan ƙasar ke yaɗa su don baiwa mutane damar dubawa ko akwai matansu, abinda ke ƙara rura wutar tashin hankalin da ake ciki, lamarin da ya tilastawa gwamnatin ɗaukar matakin takaitawa jama’a damar sauke bidiyon
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI