Bayan da zanga-zangar nuna adawa da amfani da ya wuce ka'ida da 'yan sandan musamman masu yaki da fashi da makami ke yi a Najeriya ta koma tashin hankali, jihohin Rivers da Delta da ke kudu maso-kudancin kasar sun saka dokar hana fita waje.
Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya sanar da daka dokar hana fita ta awanni 24 sakamakon yadda zanga-zangar ta juye tare da komawa rikici.
Wike ya ce a zanga-zangar da aka yi a ranar Laraba a jihar an kashe mutane 8 da suka hada da 'yan sanda 3.
Ya ce "A yayin zanga-zangar, wasu da ba a san ko su waye ba sun kona caji ofis din 'yan sanda na Oyigbo da gine-ginen kotu. An lalata dukiya da dama a rikicin da aka yi a yankin Ikokwu. Domin magance rikicin an saka dokar hana fita ta awanni 24."
Gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa ya sanar da dokar hana fita ta awanni 48, amma za a bar masu aiyukan da suka zama dole fita waje.
Okowa ya kara da cewar sakamakon rikicin, makarantun sakandire da firamare za su ci gaba da kasancewa a rufe har nan da 2 ga watan Nuwamba.