Hukumar ta ECOWAS ta lura cewa, daga cikin mutane miliyan 406 da ke rayuwa a yankin Afrika ta yamma, miliyan 208 ba sa samun wutar lantarki, sannan kusan kashi 70 na waɗanda ba su da lantarkin, mazauna karkara ne.
Yanzu haka hukumar ta ce, za ta magance wannan matsalar ta rashin lantarkin a ƙarkashin wani shirinta na ROGEAP wanda aka ƙirƙire shi musamman don wadatar da ƙasashen yammacin Afrika 15 da wutar lantarki.
Bankin Duniya da Asusun Bunƙasa Tsaftatacciyar Fasaha na CTF da Ofishin Hulɗa da Ƙasa da Ƙasa na Gwamnatin Netherlands ke ɗaukar nauyin wannan shirin na samar da lantarkin a yammacin Afrika.
A yayin da yake magana a taron masu ruwa da tsaki a birnin Abuja na Najeriya, Babban Mashawarci a Hukumar ECOWAS kan shirin na ROGEAP, El hadji Sylla ya bayyana cewa, shirin na samar da lantarkin zai laƙume dala miliyan 380, yana mai cewa, manufarsu ita ce samar da lantarkin ga makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya da zummar inganta gudanar da ayyuka.
Hukumar ta ECOWAS ta ce, za ta kammala aikin wadata waɗannan wurare da wutar lantarki cikin watanni 18 kacal.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI