Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da ECOWAS din ta fitar, tana mai cewa har yanzu kofa a bude take ga wadannan kasashe, a duk lokacin da suka sauya shawarar sake koma wa.
A cikin sanarwar, ECOWAS ta ce za a ci gaba da mutunta fasfon jama'ar wadannan kasashe uku da ke dauke da tambarin ECOWAS, hadi da katinsu na shaidar dan kasa.
Haka zalika kungiyar ta ce za a ci gaba da kallon wadannan kasashe tamkar mambobinta, har ma ta bayyana a cikin sanarwar cewa, harkokin kasuwanci tsakanin kasashe mambobin ECOWAS da kuma kasashen Nijar, Burkina Faso da kuma Mali zasu ci gaba da tafiya kamar yadda suke a baya.
Sanarwar ta kuma bukaci kasashen kungiyar, da su ci gaba da bawa jama'ar kasashen uku damar shiga kasashensu ba tare da takardar izinin shiga ba, da kuma zama, har sai baba ta gani.
Kungiyar ta ce an fitar da wannan sanarwa ne, domin kaucewa haifar da zaman tankiya ko kuma dardar tsakanin jama'ar wadannan kasashe uku, musamman 'yan kasuwa, da kuma kwantar musu da hankula.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI