ECOWAS ta kare Najeriya dangane da zargin da Nijar ke yi mata

ECOWAS ta kare Najeriya dangane da zargin da Nijar ke yi mata

Ecowas na martani ne bayan da shugaban mulkin sojin, Nijar Janar Abdourahamane Tchiani ya zargi Najeriya da samar da mafaka ga wasu Faransawa biyu da ta kora, bisa zarginsu da maƙarƙashiya ga gwamnati, wajen haifar da rikici a ƙasar yayin wata hira da aka watsa kai tsaye ta gidan talabijin ɗin ƙasar ranar kirsimeti.

Janar Tchiani ya kuma soki ƙungiyar ECOWAS inda ya yi iƙirarin cewa Faransa ta kafa sansani a Najeriya inda take bai wa ƙungiyoyin ta'addanci makamai a yankin tafkin Chadi domin tada tarzoma a kasarsa.

A sanarwar da ta fitar da yammacin Alhamis, ECOWAS ta ce zarge-zargen na Nijar ba su da tushe balle makama.

ECOWAS ta yi la’akari da yadda Najeriyar ta kwashe shekaru da dama tana taimakon ƙasashen Afirka wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro, ba ma a yammacin Afirka kaɗai ba, har ma da sauran sassan nahiyar, inda  ta bayyana irin nasarorin da dakarun haɗin gwiwa na MNJTF, wadda Najeriya ke kan gaba wajen ɗaukar nauyi ke samu, a yaƙi da ta’addanci.

Dangantaka tsakanin ƙasashen biyu na Najeriya da Nijar ta yi tsami, tun bayan da sojoji ƙarkashin jagoranci Abdurrahmane Tchiani su ka kifar da gwamnatin farar hula ta Mohammed Bazoum a shekarar 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)