ECOWAS ta caccaki hare-haren ta'addanci da aka kai babban birnin Mali

ECOWAS ta caccaki hare-haren ta'addanci da aka kai babban birnin Mali

A wata sanarwa, ECOWAS ta bayyana rashin jin  daɗin ta a game da waɗannan hare-hare, waɗanda ta ce su na barazana ga zamn lafiyar yankin yammacin nahiyar  Afrika.

Sanarwar ta kara da cewa Kungiyar ta na jaddada ƙudirinta a kan duk wani shiri da kawo zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.

A ranar Talata ce aka kai wa birnin Bamako munanan hare-hare, waɗanda ƙungiyyar nan mai ikirarin jihadi da ke da alaƙa da Al-Qaeda ta ɗauki alhakin kaiwa. Har yanzu dai  ba a bayyana adadin mutanen da waɗannan hare-hare su ka rutsa da su ba.

Birnin Bamako bai cika fuskantar hare-hare na masu ikirarin jihadi ba kamar yadda wasu sassan kasarke fuskanta kusan kullayaumin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)